Youtube channel wuri ne da ake iya adanar hoto mai motsi ko video da sauran abubuwa, sannan kana iya amfani dashi wajen tallata hajarka ko iliminka ta cikinsa.
Wannan shi ne bayanin yadda zaka buɗe naka, na musamman
1. Ka tabbata kana da Gmail account, saboda shi ne matakin farko
2. Saika ziyarci youtube.com.
3. Idan kana da Gmail akan wayarka zai buɗe kaci gaba da aikinka, idan kuma babu zai buƙaci kasa Gmail
4. Saika duba sama ka latsa wurin alamar hoto, idan kasa hoto a gmail naka, zaka ga hotonka saika taba wurin.
5. Sannan ka latsa "Create a Channel"
6. Zai tambayeka kana buƙatar buɗewa da saika tabbatar.
7. Zai baka bayananka na Gmail, naka saika gyara idan kana buƙatar canza sunan da yake, idan kuma baka buƙatar canza suna saika barshi haka.
Amma ka sani sunan da yake kan Gmail naka shi ne asalin sunanka da zai fito. Zaka iya canzawa nan take.