Yanayin da al'ummar mu, suke ciki ayau, ya zama abin Allah ya kawo mana ɗauki, ta yadda imani yayi ƙaranci azukata, ta yadda kowa yana neman damarsa akan ɗan uwa da abokin nema, rayuwa ayau ta zama ba kowa zaka saki jiki da shi ba, saboda sakacin shugabanni, ta yadda sata da ƙwacen kayan mutane ya zama abin burgewa ga matasa, musamman wayar hannu wacce yanzu kusan rayuwar mutane ta ta'allaƙa acikin waya, abubuwan da ake yi a waya ayau ya zama bashida adadi.
Abu mafi muhimmanci da akeyi a waya ayau shi ne kasuwanci da mu'amala ta rayuwa, mai kyau da akasinta, hakan tasa masu son zuciya da ƙarancin imani suke tururuwa wajen ƙwace wayoyin mutane, domin suyi amfani da wayar wajen satar kuɗinka daga banki.
Ga kaɗan daga bayanin da zaka taimaki kanka da gaggawa
ME YASA ZAKA BUƘACI KULLE ACCOUNT ƊINKA NA BANKI KO LAYIN WAYA?
Tsau-tsayi yana iya sa ka jefar da cika kayar ɗinka, ( Wallet) ko kuma asace maka ita, tana iya kasancewa akwai ATM ɗinka acikinta.
Yana iya kasancewa wayarka za'a ɗauka, ko ta faɗi, kana amfani da manhajar banki (Bank app) ko, layinka da kake karɓar saƙon baki yana cikin wayar da aka sace. Waɗannan hanyoyi guda uku cikin sauƙi za'ayi maka sata daga bankin ka wato
*. ATM CARD ɗinka
*. Layinka da kake ƙarbar saƙon banki
*. Wayarka android da kake, amfani da apps na banki
1. KULLE WAYA DA IMEI NUMBER
Zaka iya kulle wayarka ta hanyar amfani da IMEI, ko wacce iri ce ƙarama ko babba, matuƙar kana da IMEI nata, ka danna *#06#, zata baka lambobi guda 15, da su zaka shigar da ƙorafinka zuwa wurin ƴan sanda, su zasu taimaka wajen kulle wayarka, dan gudu daga ɓarayi, su waɗannan lambobi suna zuwa ajikin kwalin wayarka idan da kwali ka siya, idan kuma ba kwali to zaka ajiye su a wani wuri arubuce, kafin faruwar hakan.