Idan baku manta ba a cikin watan October na shekarar da muke chiki wato 2021 shugaban kamfanin Facebook ya bada sanarwa cewa ya maye sunan kamfaninsa da META. wannan dalilin ya jawo cece kuce game da ko wanne dalili ne ya jawo haka ko me hakan take nufi?
Saboda sanin muhimmancin kafofin sadarwa na dandalin sada zumunta ya sa nake tambayar kaina wai mene METAVERSE (META) ɗin nan?
Ita dai wannan kalmar da ta ɗauki hankali kuma za ta cigaba da zama abun tattaunawar da zaayi ta magana a kansa nan da zuwa shekaru ashirin masu zuwa, wani mafarki ne da ake yi a kan cigaban yanar gizo kuma ake kashe maƙudan kuɗaɗe domin gudunar da bincike da gwaji don ganin wannan mafarkin ko duniyar ta tabbata.
Kalmar Metaverse dai ta samo asali daga wani littafin da aka wallafa mai suna (Snowcash) a cikin shekarar 1992, mallakar Neal stephson.
Metavese sabuwar duniya ce ta imagination da kuma tafiyar zuchiya da hankali akan internet. Ita wannan kafa zata canza sadarwa daga rubutu da sako zuwa ido na ganin ido ko kuma ga fili ga mai doki.
Ta yadda zai iya yiyuwa ka zauna kayi game da wanda yake Japan ko America kamar kuna zaune kai da shi akan benci ɗaya a guri ɗaya.
Ta yadda zaka shiga meeting kamar yadda yanzu ake zoom da goggle meet ta hanyar video da audio to shi META zai zo da yanayin da zaka kasance da waɗanda ku ke meeting a guri daya kuna ganin juna (imaginary) kuma kuna exchanging ideas kamar duk a zaune kuke a cikin daki daya ta hanyar META world.
Metaverse zai zamo wani duniya da zaka sayi fili ka gina shago, na gani na faɗa ka ƙawata shi kuma kurwarka ta zauna a ciki ta gudanar da rayuwa kamar yadda ake gudanar da rayuwa a gaske.
Za'ayi games, Business, social engagement, Education da duk wani chilling da ka sani ta hanyar imagination.
Ya za'ayi hakan ta kasance?
Sanin kan ku ne yanzu idan aka tashi kakanninmu aka ce musu ana video call, instant messaging da zoom meeting ba za su yarda ba, to kamar haka META World zata kasance.
Shidai Mack Zuxkerberg tuni ya ware wasu zunzuritun kuɗaɗe domin yin bincike yadda kafar sada zumunta ta Facebook zata koma wani abu kamar META world.
1) Za'a kera AR Glasses.
2) Wrist Band
3)VR Headset domin tabbatar da samuwar Meta world.
Kamar yadda muke ganin virtual games da ake hawa wani abu Mai kamar lilo sannan a saka AR Glasses sai mutum ya gan shu cikin daji yana ta tsallake tsallake wani lokaci har ihu zaka ga wasu su na yi saboda imaginary feelings of Virtual reality, to tsarin Metaworld zai zamo kamar haka zaka saka AR Glasses kayi attending event a virtual world ko kayi meeting da mutanen America, Japan, KO kuyi Game kamar kuna tare.
Shi dai wannan tsari na Metaverse shine mafi ƙololuwar mankind discovery of civilization for Global world. Kuma yana nan tafe ko kusa ko nesa,
Sannan duk wani transaction na payment da za'ayi a METAVERSE world of virtual reality za'a biya ne da kuɗin Crypto Currency.
Kamfanunuwa da dama sun yi nisa wajen siyan sarari a cikin duniyar meta da kuma yin bincike domin bunƙasa ta.
Kamar yadda muke ɓata lokaci a kan yanar Gizo haka ake tunanin mafi akasarin rayuwarmu sai mun fi gudanar da ita a Metaworld fiye da reality world.
Allah shine masani.