Yanzu haka tuni an fara ƙirgen lokacin da za'a kammala gyaran project din Safemoon zuwa Safemoon V2 sai dai ba'a bada hakikanin kwanakin da za'a kaddamar da V2 din ba, kamar yanda suka alamta hakan inda aka kara jimlar “V2 coming soon” a gaban sunan dake shafin tuwita.
Shugaban Project din na safemoon John Karony shine ya fitar da bayanan wannan gyara da ake kan yi a yanzu haka, sannan ya bayyana cewa an yi sauye sauye da dama ga ɓangaren shugabancin token din, wanda har Chief Blockchain Officer (CBO) wato Thomas Smith aka sauya duk dai a shirin tunkarar gyaran da za'a yi masa.
Menene Safemoon V2?
Ta yiwu mai karatu yana so ya fahimci hakikanin gaskiyar wannan sauyin da kuma ita kanta ma'ana da amfanin wannan sauyi da za'a yi masa.
To Safemoon V2 da za'a sauya ba wai zai rage total asset din daka mallaka bane ko kuma wani gibi na market cap din sa gaba daya. Sai dai me, shi safemoon za'a rage masa yawan Supply ne da zummar kakkaɓe wancan yawan zeros din da kuma Supply nashi.
Hakan yana da amfani sosai a project ko investment asset, wanda duk ana yin sa ga wadanda ake trading nasu a irin su Stock Index, Nasdaq d.s.s
A Kai tsaye Consolidation din da za'a yima safemoon bawai irin wanda ake yi wa sauran asset din dake cikin Stock Index ko Nasdaq bane, sai dai za'a dan yi kwaskwarima ne kwatankwacin wancan gyara.
Shi gyara na consolidation din da za'a yima safemoon zai bi turbar target na token din ne gaba daya wato ya shiga kasuwannin dunuya na Crypto ta yanda zai yi mubaya'a ga pairs din Bitcoin da za'a yi kasuwanci dashi.
A takaice dai consolidation din na nufin ta yawan zeros din safemoon, amma ba za'a rage wa kowa abinda ya mallaka ba. Kamar yanda suka ce za'a tsuke shi ne kamar haka:
✌️ 1000:1 — Wato duk guda 1,000 na Safemoon zai koma guda 1 a Safemoon V2.
Maslan idan ka Mallaki Safemoon 1,000,000 to zai koma guda 1,000 a Safemoon V2.
Idan Safemoon Circulation Supply nashi 575 Trillions to Safemoon V2 zai koma 575 Billions.
Idan ka mallaki guda 1,000,000 na $10 a Safemoon to zai koma guda 1,000 kuma na $10 a Safemoon V2.
Idan akai masa hakan to manyan kasuwannin Crypto zasu karbe shi domin masu trading da BTC zasu yi amfani dashi dama sauran Altcoins.
Can't you imagine!
👉🏿 SAFEMOON/BTC
👉🏿 SAFEMOON/ETH
👉🏿 SAFEMOON/BNB
Wannan shine aikin da ake yima kuma tuni sun gama 70% nashi.
Lalle Safemoon indai an masa wannan gyaran kuma ya kammala muna da kyawawan albishirori ga re ku masu holding nashi - amma fa da Long term holder nake.
Ga ƙarfin Project, ga ƙarfin community, ga ƙarfin Holders (Over 2.5 Millions Holders) Bscscan, me kake tunani...?
A Rubutu na gaba zamu yi bayanin hanyar da za'a bi domin juya tsohon safemoon zuwa sabon Safemoon V2, ayi sharing domin yan uwa su amfana.
Subscribe Now
Thanks for Subscribing