Wannan darasi bamuyi dan mu koyar da zalinci ba, munyi shi ne, domin faɗakar da al’umma su san yadda ake, kuma su fahimci gaskiya cikin ayyukan masu zalinci, musamman yadda al’umma muka raja’a akan zalinci.
Wannan matsala ta tura kuɗi na bogi ga ƴankasuwarmu anyiwa wasu dayawa, kuma ba komai ne yasa ba, saboda saurin amincewa da Bahaushe yake da shi. Zamu kawo hanyoyi akalla guda biyar domin al’umma su fahimci wannan matsala.
Kar kayi amfani da wannan salo ka cuci wani, domin idan kayi to tabbas bamuda alhaki akan abinda ka aikata, mun gabatar da wannab darasi ne, domin al’umma su guji azzalumai.
Akwai hanyoyi dayawa musamman na applications masu yawa da ake yin wannan transfer ta bogi, zamu ɗauki apps waɗanda akafi yi dasu
Kuma duk wani apps da ake tura saƙon taro, ko na kamfani wato “Bulk SMS” to ana iya amfani dasu a wannan bangaren.
Domin ci gaba da karatu kasance da Duniyar Waya