--------------------------------------------------------------
1. A wani lamari mai kama da almara, wani Dan Dandatsa (Hacker), ya yi kutse cikin shafin cibiyar hada-hadar kudaden kirifto (Cryptocurrency) na kamfanin Poly Network a ranar talatar makon jiya, inda yayi awon gaba da nau’ukan kudaden kirifto guda 12 da kimarsu ta kai dalar Amurka miliyan 610 ($610 mil), kwatankwacin naira biliyan 302.10 (N302.10bn).
2. Wannan, a cewar masana harkar kirifto a duniya, ita ce sata ta hanyar kutse mafi girma da muni, a tarihin hada-hadar kudaden zamani na Intanet, wato: “Cryptocurrency”.
3. A cewar Kelvin Fichter, mai fashin baki kan harkokin kudaden zamani na Intanet kuma masani a tsarin gina manhajar “Cryptocurrency”, “Dan Dandatsan ya yi amfani da kwarewarsa ne wajen goge bayanan tantancewa (Smart Contracts Calls) da kamfanoni uku (Binance SC, da Etherium, da kuma Polygon) ke amfani dashi a manhajarsu, sannan ya maye gurbinsu da nasa adireshin asusun.”
4. Ganin haka yasa kamfanin Poly Netowork ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga dan Dandatsan da ya aiwatar da wannan kutse, yana mai sanar dashi cewa: “Ka sani, wannan zunzurutn kudade da ka sace ta hanyar kutse, shi ne adadi mafi yawa a tarihin hada-hadar kudaden kirifto a duniya. Kudaden da ka sace (har wa yau), kudaden dubunnan mutane ne da ke hada-hada a wannan mahalli. Ya kamata mu fara tattaunawa da kai, don samun mafita.” A karshe sakon yaci gaba da cewa: “Amma idan kaki yarda, to, ka sani abin da ka aikata laifi ne mai girma, wanda za a iya hukunta ka a kai, a kowace kasa ce kuwa.”
5. Aika wannan sako ke da wuya, sai wannan dan Dandatsa ya fara dawo da wani adadi ko kaso na kudaden da ya sace, inda a tsakanin sakon ya sanar da cewa: “Na amince, zan dawo da wadannan kudade gaba dayansu. Amma kafin nan, a sanar dani adireshin taskar da zan aika kudaden gaba daya. Daman na yi hakan ne ba don zalunci ba, sai don nuna wa masu wannan cibiya irin kura-kuran da madaukan hada-hadar kudadensu ke dauke dashi. Ban yi haka don guduwa da kudaden ba.”
6. Abin mamaki, nan take yaci gaba da ingizo wadannan nau’ukan kudade da ya wawashe, kadan, kadan; lokaci bayan lokaci. Kwanaki biyu bayan wannan tabargaza, dan Dandatsar ya dawo da adadin kudaden da kimarsu ya kai dala miliyan 325 ($325 mil). A duk sadda ya ingizo kudade, kamfanin Poly Network kan fitar da sanarwa mai dauke da adadin kudaden da ya ingizo, da kuma lokacin da ya ingizo.
7. A halin yanzu ya aiko ragowar kudaden a cikin adireshin asusun da aka bashi, amma yaki mika kalmar sirrin da za ayi amfani da ita wajen mallakar ragowar kudaden. Ana dai jiransa.
8. Wata badakalar sai Intanet!