X56K1bsIiGVjkxmVJNQ5

ƘWACE FACEBOOK ACCOUNT YAYI YAWA



1. Idan da lambar waya ka buɗe ka ɓoye lambar wayarka, ta zama "Only me"

2. Haka idan da email ka buɗe, shima ka ɓoye ta ya zama kai kaɗaine mai ganinta.

3. Ba'a saka password mai sauƙi, idan naka lambar waya ne, ko sunanka ka canza misalin da ake buƙata na password kamar haka "WA2021ya" ko 20Wa21yA, ya zama mai rikitarwa.

4. Idan zaka canza waya ka tabbata ka goge kanta duka, shi ne mafi sauƙi.

5. Ka rage amfani da Keyboard themes ko Launcher marar tabbaci balle inganci.

6. Karka kuskura wani ya kiraka yace yayi kuskuren turo lambobi kan layinka, kowa layinsa daban, haka Code ɗin wani layin baya yiwa wani layin, da zarar ka bawa wani code ɗin to naka za'a ƙwace.

Please Select Embedded Mode For Blogger Comments

Previous Post Next Post