X56K1bsIiGVjkxmVJNQ5

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA UKU

Fotolia

“Fotolia” ko kuma “Adobe Stock” a yanzu. Shafin da kuka sani a matsayin Fotolia a dori yanzu ya canza suna zuwa Adobe Stock.

Idan ka kware a daukar Hoto, Bidiyo, Yin Zane ko zanen 3D ko kuma “Templates” da za’a iya saraffawa ayi wani aiki dasu kala dabam-dabam to tabbas Fotolia ce hanya mafi sauki da zaka saida wadannan hotunan masu kayatarwa da ka dauka ko ka zana. Sai dai dole ka kasance ka wuce shekara 18 sannan dukkan abubuwan da zaka daura su zamana mallakin ka ne.

Akwai ‘yan kasuwa da dama da wakilan kamfuna da suke neman irin wadannan abubuwan domin wallafe-wallafen su ko kuma sakawa a shafinsu na yanar-gizo, idan sukaci karo da aikinka kuma yayi daidai da abunda suke bukata to tabbas zasu biya domin suyi amfani dashi.

Domin farawa abunda kawai kake bukata shine ka shiga wannan shafin ka buda taskarka (Account Mallakinka) domin ka fara daura kayanka. Daga nan duk wanda ya gani kuma yanada ra’ayi zaiyi aiki da Fotolia ya biyaka sannan ya samu yayi amfani dashi kai kuma zaka dinga ganin abunda ka tara a allon bayanai na taskar ka. Duk lokacin da wani ya saye to zaka ga samunka ya karu.

Duk abunda ka sayar zaka samu naka kaso, idan ka sayarda hoto ko zane ko tsagwaron fayil na zane wanda za’a iya sarrafawa to zaka samu kaso 33% daga ciki sannan idan ka sayarda bidiyo zaka samu kaso 35%.

Da zarar kudinka yakai $25 ko N9,600 zaka iya cirewa ta hanyar amfani da PayPal ko Skrill.

Zaku iya shiga Fotolia kuma ku ci wannan gajiyar ta wannan link: https://contributor.stock.adobe.com/en/onboarding/sync-fotolia-1

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Swagbucks.

Please Select Embedded Mode For Blogger Comments

Previous Post Next Post