RUBUTU: KASHI NA HUDU
Swagbucks
Swagbucks shine shafin da yafi kowane shafi shahara da kuma samun amincewar mutane wajen biyan kudi domin yin kananan abubuwa a cikin shafin kamar:
* Kallon bidiyoyi musamman masu tallace-tallace
* Bada amsa ga tambayoyin jin ra’ayi (surveys)
* Sayyayar kaya a shagunan yanar-gizo (online-shopping)
* Binciken shafukan yanar-gizo (web searching) domin zakulo wasu bayanai.
* Gayyatar abokai domin su shigo cikin tsarin (referrals)
Duka wadannan ayukkan ana biya idan kayi dai daga cikinsu saidai Swagbucks yazo da wani tsari na daban, saboda suna biya ne da Swagbucks Point (SB), su kuma wadannan “points” din duk guda dari (100) waton 100SB a matsayin dalar Amurka daya ($1) suke.
Abin burgewa gameda Swagbucks, zakayi abubuwan da ka saba yi ne kuma a biyaka. Alal misali, Da yawanmu mukan shiga Google ko Bing muyi bincike da na’urar bincikensu domin samun wani abu, to idan kayi bincike da na’urar bincike ta swagbucks biyanka za’ayi. Haka, Mukan shiga YouTube mu kalli bidiyo, to idan ka kalli bidiyon Swagbucks biyanka za’ayi.
Swagbucks sunada hadin guiwa da manyan shagunan yanar gizo kamar su Amazon da Walmart da sauransu fiye da shaguna 1500. Idan kabi ta hanyar Swagbucks kayi sayayya a wadannan shagunan to zaka samu “SB Points” daidai sayayyarka.
Gameda amsa tambayoyin jin ra’ayi (surveys) suna da sauki sosai kuma sunada “SB Points” da yawa, kullum kana iya amsa tambayoyi dayawa kuma ka tara kudi da yawa daidai kwazon ka.
Har wa yau, Swagbucks sunada wani shafi da ake kira “Discover Offers” ko “Discover Deals” waton shafin samun damar-maki. Idan ka buda taska (Account) da Swagbucks kuma kayi nasarar shiga cikin shafin to a cikin wannan shafin zaka samu wasu damar-maki dayawa, zaka dinga ganin abubuwan da zakayi su baka SB Points masu yawa da kuma wasu ababen shaguna da aka rage wa farashi. Misali: akwai tambayar jin ra’ayi da zaka samu SB 15 to a cikin “Discover” zaka iya samun SB 100 gareta. Haka kuma, akwai abunda Amazon ko wani shago zasu saka a farashin dala $5 amma a cikin shafin “Discover” na Swagbucks zaka iya samunshi a dala $3 ko $3.5.
Da zarar kudinka suka kai adadin da za’a iya cirewa to zaka iya cirewa ta PayPal ko kuma GiftCards.
Wannan shine takaitaccen bayani gameda Swagbucks. Domin samun wannan dmar zaku iya shiga swagbucks kuma kuyi rajista a kyauta ta wannan link https://www.swagbucks.com/p/register?rb=76586833
Allah yasa mu dace!
Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Skillshare.