X56K1bsIiGVjkxmVJNQ5

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA 127,000 DUK WATA


RUBUTU: KASHI NA BIYU

Fiverr: tabbas nasan kunsha jin wannan zancen “idan ka kware akan wani abu to kada kayishi a kyauta” to wannan shine aikin da Fiverr zai maka, idan kasan ka kware akan wani abu to tabbas kayi rajista da wannan shafin.

YA FIVERR YAKE AIKI?

Wannan abu ne mai sauki.

Idan kasan ka kware akan wani abu irin Zane ko Editin din hoto, Zana shafin sadarwa, samarda manhaja, hada sauti, bidiyo ko rubutu da dai sauransu to Fiverr shine babbar hanyar da zakayi amfani da ita wajen samun kudin shiga da sayarda wannan fasaha cikin sauki.

Matakin farin zakayi rajista da Fiverr wanda yake kyauta ne daga nan sai ka kirkiri abunda ake cema “gig” wato fasahar da kake so ka saida zuwa ga kwastomominka.

A Fiverr zai iya yimaka wuya wajen samun kwastomomin farin saidai Insha Allah idan ka karanta wannan rubutun zai zamo maka da sauki sosai wajen samun kwastomomi.

Kwastomomi a Fiverr suna duba tsokaci (Review) da aka aikewa mai aiki (Freelancer) da kuma awon-inganci (Rating) da akayi akan ayukkan ko wane mai aiki kafin su fara bashi aiki. Saboda haka dole ka jajirce kayi ayukka masu kayatarwa da za’a yaba.

A Fiverr akwai wani tsari da ake kira “Gig Extra” ta wannan tsarin zaka iya tara wasu kudi masu yawa bayan kudin aikinka. Yanda “Gig Extra” ke aiki shine: alal misali kana harkar zana shafukan sadarwa kuma ka saka cewa a cikin kwana 5 ko 7 kake kare aiki idan an baka, sai wani kwastoma yazo yace yana son aikin cikin kwana 3, to a nan “Gig Extra” zai baka dama ka cajeshi wasu kudi bayan na aikinka kamar yadda ka saba.

Fiverr nada dadin aiki sosai kuma zaku iya tara ko nawa a wata kuma zaka iya debe kudinka ta amfani da katin ATM “credit ko debit card”domin cire kudinka.

Zaku iya shiga kuma kuyi rajista a Fiverr ta wannan hanyar http://www.fiverr.com/s2/d6bd8786c3

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Fotolia.


Please Select Embedded Mode For Blogger Comments

Previous Post Next Post