RUBUTU: KASHI NA BIYAR
Skillshare
Tabbas kanada wata baiwa. Hakika nasan akwai wata Baiwa ta wani ilimi da Allah ya hore maka wadda idan ka sanarda wani ita, to zai samu cigaba a rayuwa. Idan kasan kanada wannan baiwar kuma kanada dabarar da zaka koyama wasu ita cikin faifan bidiyo, to wannan ne lokaci mai kyau da ya kamata kashiga Skillshare.
Tsarin Skillshare tsari ne mai kyau sosai da kuma Inganci. Akwai sauki a wannan tsarin kwarai dagaske, ana samun kudi sosai sannan kuma ana amfanar da mutane.
Ya Skillshare yake aiki?
Idan kanada wani abu dakake iya koyarwa to Kawai zakayi rajista ne sai ka shirya ka dauki wannan karantarwa ta hanyar bidiyo sai ka daura bidiyon a Skillshare daga nan zaka fara samun kudi ba tareda ka sake wani aiki ba.
A Skillshare akwai dubbanin dalibai da suke koyon kwasa-kwasai kala daban-daban kama daga dubarun kasuwanci, Zane, Kimiyya, lissafi da sauransu.
Ta wannan hanyar su kuma malamai suna koyarwa suna samun kudi abun su. Abin burgewa ga Karantarwa a Skillshare babu bukatar wani kwali ko takarda domin fara karantarwa, idan kasan ka iya kawai kayi sai ka daura, ana kallawa kana samun kudi, Dalibai na kara kallawa kana kara samun kudi.
A Skillshare akwai wasu Dalibbai da ake kira “Premium Students” to wadannan dalibban suna baka damar kara samun kudi sosai. Duk lokacinda “Premium Student” ya kalli bidiyo dinka na tsawon minti talatin (30mins) to za’a biyaka kudin wannan watan.
Iya tsawon mintuna da aka kalli bidiyo dinka iya kudin da zaka samu. Bayan kayi rajista, kanada damar gayyatar abokananka zuwa Skillshare kuma duk mutum daya yayi rajista da link dinka to zaka samu dalar amurka ($10) dai-dai da N3,873.
Akwai masu koyarwa a Skillshare dayawa da suke samun kudi kimanin dalar amurka $300 zuwa dala $100 kwatankwacin N116,200 zuwa N387,310 kowane wata. Wannan ba karamar dama ba ce, da fatar zamu gwada domin muci wannan gajiyar.
Zaku iya yin rajista a Skillshare ta wannan link https://skl.sh/2ZV5y3L
Allah yasa mu dace!
Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan “Get Paid for Being Someone’s friend (RentAFriend).