RUBUTU: KASHI NA SHIDA
RentAfriend
Amma akwai ban mamaki a wannan al’amarin, ta ya zan samu kudi kawai saboda na zamo abokin wani. To saurara kaji, wannan na faruwa ne kawai a RentAFriend.com
Wannan wani tsari ne da zaka iya hayar aboki a lokacin da ka shiga wata kasa ko gari kuma baka san kowa ba, to idan kayi rajista a RentAFriend zaka samu damar da zaka iya daukar wasu haya kuma su su yi maka abinda kake bukata ka biyasu. To a wannan zaka samu kudi idan wani ya daukeka haya.
Abubuwan da zaka iya yiwa wanda ya nemeka abota a RentAFriend:
* Yawon Shakatawa
* Kallon Fim
* Rakkiya zuwa cin abinci a wata restaurant
* Rakiyya zuwa wurin buki ko wani taro
* Koyarwa akan al’ada ko wata dabi’a
* Nuna masa gari ko kauyuka
Wannan shafin an tanadeshi ne kawai saboda abota da taimakawa abokantaka da abubuwan da aka lissafa. Ba zaka iya aiki dashi ta wasu hanyoyi na soyayya ko makamancin haka ba, duka an haramta wannan a RentAFriend.
Idan kanada ra’ayin aiki da wanna shafin kuma kanada gurin samun kudi dashi to kawai kaje kayi rajista a shafin, ka cike Sunanka, Adireshinka, Ra’ayinka, Lambar waya da za’a iya kiranka ko turama sako da wasu sauran bayanai sannan ka saka hotonka, duk lokacinda wani yazo ya duba yaga yanada ra’ayi dakai to zai nemeka ko ya kira wayarka ko ya turama sako ko kuma ya tura maka sako ta cikin sashen tattaunawa da RentAFriend suka tanada.
Idan aka gayyace ka, kana iya cajin wanda ya gayyace ka daga dalar amurka goma ($10 — N3,874) ko fiye da haka, ya danganta da irin yanayin aikin da yake bukata da kuma lokacin da za’a bata. Idan kuma biki ne ko wani taro zaka iya kara farashi.
zaku iya shiga RentAFriend ta wannan link: rentafriend.com
Allah yasa mu dace!
Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan “StartProofReading”.