X56K1bsIiGVjkxmVJNQ5

Kana da bukatar yin bincike na aƙalla mintuna 30 zuwa 40 ko fiye da haka, kafin siyan kowanne sabon Coin/Token.

Ba daidai bane kawai wani yace maka kaje ka sayi Coin kaza, kawai ka dauki kudadenka ka zuba ba tare da tabbacin inda ka sanya su ba.

Ka tuna irin wahalar da kasha kafin ka samu kudin ka, to kada ka saka a inda zaka yi asara.

Crypto currency zai iya mayar da kai DANGOTE a dare daya, haka kuma zai iya mayar da kai KAMAYE a dare daya.

Ka da ka zauna haka sakaka, in dai kana Son cin moriyar harkar Crypto, dole sai ka tashi haiƙan ka nemi ilimin harkar.

Kada ka tsaya kana jira sai ance maka siya, siyar, ajiye, da sauransu. Wasu ma sai sun jira wani ya siya musu Coin din ya tura musu. To In sai an siya maka, In kuma zaka siyar ya zaka yi?

Allah ya bamu sa'a.

Please Select Embedded Mode For Blogger Comments

Previous Post Next Post