Sanarwar da Shafin Gonar Bitcoin ya samu ta bayyana cewar LISSAFIN ADADIN Safe Game Cash da duk wani mai rike da SAFEMOON cash zai samu ya dogarane da bangarori guda biyu na farko asalin TOTAL SUPPLY na SAFEMOON CASH da kuma TOTAL SUPPLY na Safe Game Cash.
Ga yadda lissafin zai kasance:
TOTAL SUPPLY na SAFEMOON CASH 100 QUADRILLION ne wato lamba daya da 1 da ZERO 17 (1000,000,000,000,000,00).
A yayin da shi kuma SAFEGAME cash TOTAL SUPPLY nashi zai kasance ONLY 1 QUADRILLION wato lamba daya da ZERO 15 (1000,000,000,000,00) an cire ziro biyu kenan.
Me wannan LISSAFIN yake nufi?
A takaice dai abinda hakan ke nufi shi ne duk Safe Game Cash guda daya dai-dai yake da Safemoon cash guda 100.
Domin a TOTAL SUPPLY dinsa gaba daya an cire ZERO BIYU an barshi 1 QUADRILLION madadin 100 Quadrillion na shi ainihin SAFEMOON CASH.
Don haka ko Safemoon cash nawa gareka to kawai ka cire ZERO guda biyu.
Idan kana da guda Biliyan 25 ( 25000,000,000) to ka cire ZERO BIYU zai zama cewar za'a baka Safe Game Cash guda MILIYAN 250 haka zalika idan misali ace kana da guda miliyan dayane to ka cire ZERO BIYU zai zama cewar za'a baka SAGE GAME CASH guda dubu goma kenan.
Idan Safemoon cash din ka guda dubu uku ne 3000 to ka cire ZERO BIYU. Zai zama za'a baka SAFE GAME CASH guda 30 kenan.
TO AMMA IDAN MISALI ACE SAFEMOON CASH DINA GUDA BILIYAN 25 NE KUMA YANA NUNAMIN DALA (50) AMMA KUMA YANZU AN KARBESHI AN BANI SAFE GAME CASH MILIYAN 250 SHIKUMA DALA NAWA ZAI KAMA?
Musayar da za'ayi maka bazai shafin DARAJAR TOKEN dinka ba. Yawan sane kawai zai banbanta amma DARAJAR sa zata kasance yadda ya KAMATA.