Crypto kalmace ta turanci wadda take nufin Abin da ke da tsaro , wato a bin da aka bashi tsaro kokuma ince aka tsareshi.
Crypto Currency ko kuma digital Currency a wani bangaren yana nufin kudi amma na lantarki , Kudade kamar kowanne irin kudi amma su ba a ganin su da ido (kamar yadda baka ganin kudade azahiri)a kan internet suke kuma ana saye da sayarwa da su ana iya canjasu zuwa kudi da muke amfani da su yaudakullum kamar NAIRA , URO , SAIFA dadai sauransu .
Nasan zakayi mamaki danace kudin lantarki wanuma zai'iya cewa wannan ai shirme ne , Sai in ce " karamin misalin da zan iya baka shine " , Yanda kake sa kudi a banki daga bisani su rikide su zama numbobi ko kuma a turo ma numbobin daga wani wuri kuma ka iya cire su haka Crypto Currency yake sai dai crypto currency yana da tsaron da banki basu da shi domin kuwa ba a iya hacking nashi , shi yasa ma ake kiran su da crypto hakan na faruwa ne saboda amfani da ake yi da wata fasahar zamani maisuna BLOCK CHAIN.
Da akwai Ire-iren wadannan kudaden na na lantarki wato crypto currency suna da yawa sosai amma shahararru daga ciki sune (1) Bitcoin(BTC).
(2) Ethereum (ETH).
(3) Litcoin (LTC).
(4) Bitcoin Cash (BCH).
(5) Binance Coin (BNB)
(6) FreeCoins
da dai sauran su.
Wadannan kudaden suna da matukar daraja domin kuwa a yanzu haka Bitcoin daya ya kai kusan Milyan 20 da wani abu.