RUBUTU: KASHI NA GOMA - NA KARSHE
YouTube
Kamar yada muke kallon YouTube a matsayin wata kafa ta kallon bidiyo, ko alama YouTube ba nan kadai ya tsaya ba. YouTube ma karan kanshi wata manhaja ce ta bincike (Search Engine) wadda Google kadai ke gabanta kuma a halin yanzu YouTube nada mabiya masu aiki dashi duk wata fiye da biliyan daya da miliyan dari tara (1.9 billion active users).
A nawa tunani mutane dayawa sun san yadda YouTube yake aiki da kuma yadda ake samun kudi daga manhajar. Idan kanada bukatar Karin bayani akan yadda YouTube yake aiki to ga bayanin a kasa.
Idan yau zaka shiga YouTube to kana bukatar yin rajista sannan ka buda tasha (channel) wadda zaka dinga daura bidiyoyi a kanta. Yanada kyau ka ba tashar ka maudu’i guda mai kyau. Alal misali: Tashar bidiyon kasuwanci, Tashar Bidiyon abinci, Tashar bidiyon Kimiyya da sauransu.
Ya zaka fara samun kudi a YouTube?
Idan ka buda Tasha kuma ka daura bidiyoyi har ka samu akalla mabiya dubu daya (1000 subscribers) da kallo na awa dubu hudu (4000 hours of watch) to zaka iya neman a fara biyanka (monetization) ta hanyar Google Adsense.
A halin yanzu akwai dimbin mutane da suke ta fadi-tashi domin ganin sun samu Mabiya (subscribers) da Masu kallo (viewers) domin ganin sun kara samun kudin shiga.
Domin samun kudin shiga masu tsoka dole sai ka dinga samun masu kallo sosai a wata. Domin samun masu kallo sosai a wata kanada hanya biyu:
* Ta daya: ka daura bidiyo wanda mutane suke nema sannan kayi Addu’a domin ya yadu sosai, ta hakan zaka iya samun mabiya (subscribers) da masu kallo (viewers) masu yawa.
* Ta biyu: ka daga darajar bidiyon ta hanyar “YouTube Search Engine Ranking” ta yadda mutane zasu dinga ganin bidiyon ka a yayinda suke ja suna duba bidiyoyi (scrolling and watch) ko kuma lokacin da sukayi kokarin neman (search) wani bidiyo makamancin naka.
A wadannan hanyoyin guda biyu ta daya batada wuya sosai amma ta biyun dole sai ka samu ilimin “YouTube SEO” domin bidiyoyinka su dinga yi sama ta hanyar amfani da kalmomi “keywords”.
Daga wannan ya faru to zakaga bidiyon ka na ta samun daukaka ta yanda zaka samu kudi sosai ta hanyar tallace-tallace da zasu dinga daurawa a shafinka ana biyanka.
Zaku iya dauko Manhajar YouTube a Playstore ko Appstore.
A kula: duka shafuka da na kawo guda goma a rubuce-rubucen da nayi a baya da wannan na gaba bawai shafuka ne da zasu sa ka zamo mai kudi a dare daya ba. Shafuka ne dake bukatar aiki, lokaci, hakuri da jajircewa. Idan ka dage ka sa wadannan abubuwa guda Hudu Insha Allah zaka dace. A tuna, babu wata hanya ta kwarai da zaka samu kudi ba tare da kayi aikin komai ba.
Allah yasa mu dace!
Wassalamu Alaikum Warahmatullah.