RUBUTU: KASHI NA TARA
Amazon Associates
Amazon Associates ko Amazon Amazon Affiliates tsarin hadin guiwa ne da Kamfanin Amazon wanda yake mallakar Jeff Bezos ne mutumin da yafi kowa kudi a duniya a halin yanzu.
An shirya wannan tsarin ne domin samun riba tsakanin kamfanin da kuma mutanenda ke cikin wannan shirin. Ribar kamfani itace zaka tallata kayansu domin a sayar kai kuma ribarka itace kudin da za’a biyaka.
Ya wannan shirin ke aiki?
Wannan tsarin kama daga shigar shi har zuwa yanda yake aiki abu ne mai sauki sosai. Idan kanada ra’ayi da wannan tsarin kawai zakaje ne kayi rajista daga nan zasu baka “referral link” kuma shi wannan “link” din akwai “referral Id” naka a cikinsa ta yanda duk lokacin da wani ya tabo wannan link din to zasu gane cewa daga gareka yazo kuma duk abunda ya saye zaka samu naka kaso daga sayayyar da yayi.
Abu biyu da suke abin burgewa ne sosai a wannan kasuwancin:
* Na daya: abunda ake bukata ya zamana kanada BLOG ko Mobile App kafin fara wannan aikin amma idan kanada YouTube Channel itama zatayi lafiya kalau. Haka kuma, idan kanada Account a Facebook ko Twitter to zasu taimaka maka sosai wajen tallata kayan saidai idan kanada shafin da mutane ke biya sosai to zaka fi samun riba mai yawa.
* Na biyu: duk lokacinda ka tallata wani abu sai wani yabi ta link din to koda bai saye wannan abin ba to zaka samu naka kamisho. Misali: idan ka tallata Talabijin sai wani yabi tallar amma bai sayi talabijin din ba, kawai sai yaga wata salula ta birgeshi sai ya siya to zaka samu kaso a wannan salular da ya saya.
Idan kanada blog ko tashar YouTube da ake biya sosai to cikin sauki zaka iya samun dalar amurka dubu daya $1000 a wata, kwatankwacin N387,500.
Zaku iya shiga Amazon Associates ta wannan link https://affiliate-program.amazon.com/home
Allah yasa mu dace!
Rubutu na karshe zaizo bada jimawa ba akan YouTube.