X56K1bsIiGVjkxmVJNQ5

CIKAKKEN ABAYANI AKAN SOFTWARE DA HARDWARE

*Assalamu alaikum barkan ku da wannan lokaci*

Yau insha Allahu zamu yi bayani ne akan *software* , du da cewa mun san wasu sun san software amma kuma akwai waɗanda har yanzu basu gama fahimtar mene software ba.

To da farko dai Software shine abubuwan da kwamfuta da wayar hannu suke buƙata domin yin aiki, haka kuma software shine abubuwan da muke buƙata don yin kowane aiki a cikin kwamfuta ko wayar hannu. Irin waɗannan ayyukan da muke yi sune kamar kallon bidiyo, sauraron sauti, yin game, yin rubuce-rubuce, shiga yanar gizo, da sauran dukkan ayyukan da muke yi a cikin kwamfuta ko wayar hannu duk muna yin su ne ta amfani da software. Wannan ne yasa matuƙar babu software to kwamfuta ko wayoyin hannu ba zasu iya yin komai ba, haka kuma muma ba zamu iya yin komai da waɗannan kwamfutoci da wayoyin hannu ba.

Idan kuka duba zaku ga cewa gaba ɗaya abubuwa guda biyu sune suka haɗu suka  zama computer, wato Hardware da kuma Software. Hardware sune  abubuwan da muke iya gani kuma muke iya taɓawa. Yayin da Software kuma sune abubuwan da muna iya ganin su ne kawai a cikin kwamfutar amma ba zamu iya taɓawa ba, kuma sune suke bamu damar yin amfani da kwamfuta tare da yin ayyukan da muke buƙatar yi cikin kwamfutar.

Duba da buƙatun masu amfani da kwamfuta da kuma kwamfutar kanta an raba software zuwa nau'ika biyu, nau'i na farko shine *System Software# , nau'i na biyu kuma shine *Application Software* .

*System Software* sune waɗanda computer take buƙatar su domin yin aiki yadda ya kamata. Nau'in waɗannan software ana buƙatar su a cikin kwamfuta kodayaushe kuma dole ne su kasance suna gudana a kowane lokaci domin cigaba da aikin kwamfutar. Haka nan suma waɗannan software sun rabu iri daban-daban, sun haɗa da *Operating System, Device driver, Firmware, Utility program,* da kuma *Translator* .

Inshaallah nan gaba zamu yi bayani game da waɗannan system software guda 5 da muka lissafa.

*Application Software* kuma sune waɗanda masu amfani da computer suke buƙatar su domin yin aikace-aikace a cikin kwamfutar. Nau'in waɗannan software aikin su shine bawa mai amfani da kwamfuta damar yin ayyuka daban-daban waɗanda yake buƙatar yi acikin kwamfutar. Haka nan suma waɗannan software sun rabu zuwa *General Purpose Application Software* da kuma *Special Purpose Application Software*.

*General Purpose Application Software* sune waɗanda kowa yana iya amfani dasu a ɓangarori kamar kasuwanci, ma'aikatu, ofisoshi, da sauran wuraren aiki.  Misali: (Media players da ake amfani dasu domin kallon bidiyo, sauraron sauti, duba hotuna da sauran su), (Editor da ake amfani dasu domin gyaran videos, audioa, images da sauran graphics), (Word processor da muke amfani da su domin yin rubuce-rubuce kamar Ms Word, WPS office, Open Office Writer, Word Perfect, Google Doc da sauran su), (Web browsers da ake amfani da su domin shiga yanar gizo kamar Chrome, Microsoft edge, Firefox, Safari, Opera mini da sauran su),
 
*Special Purpose Application Software* kuma sune waɗanda aka keɓance su, ko aka iyakance su zuwa ga wasu ɓangarori na musamman. Misali: (Accounting Management Software domin aikace aikacen kula da harkan kuɗaɗe), (Payroll System Software), (Banking Software domin gudanarwa da tafiyar da harkokin banki), (Hospital Management Software domin aikace-aikacen kula da asibiti),
(Attendance System Software), (Billing System Software) da sauran software irin waɗanda manyan ƙungiyoyi da kamfanoni ne suke buƙatar su.

👉  *Idan akwai mai tambaya sai yayi*








Please Select Embedded Mode For Blogger Comments

Previous Post Next Post